Bayan da sojojin Masar suka tsige Mohamed Morsi daga mukaminsa na shugaban kasa a watan Yulin shekara ta 2013, tsagerun masu tsattsauran ra'ayi sun kafa babban sansaninsu a zirin Sinai, da kaddamar da hare-hare da dama kan sojoji da 'yan sanda, lamarin da ya hallaka tare da raunata daruruwan mutane.
Shugaban hukumar leken asirin soja na kasar Masar Mohamed Faraj, ya bayyana a ranar Juma'ar data gabata cewa, tun da lokacin sojojin kasar suka kaddamar da gagaruman ayyukan murkushe 'yan ta'adda a watan Satumbar shekara ta 2015, zuwa yanzu, sojojin sun yi nasarar hallaka 'yan ta'adda kimanin 500 a zirin Sinai.(Murtala Zhang)