in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An samu kayan fashewar bom a wasu gawawwakin fasinjojin jirgin sama na Masar da ya yi hadari
2016-12-16 13:56:06 cri
A jiya Alhamis 15 ga wata ne, hukumar kula da zirga zirgar jirgin saman fasinja ta Masar ta ba da sanarwar cewa, an gano alamun fashewar bom a jikin wasu gawawwakin fasinjojin jirgin saman kamfanin jirgin saman Masar samfurin MS804 da ya yi hadari.

Sanarwar ta ce, kwamitin bincike game da hadarin zai mika rahoto kan wannan batu ga babbar hukumar gabatar da kararraki ta kasar.

A safiyar ranar 19 ga watan Mayun bana ne, jirgin saman fasinja kasar Masar samfurin MS804 da ya tashi daga Paris na Faransa zuwa Alkahira na Massar ya yi hadari, inda mutane 66 da ke cikinsa suka halaka.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China