in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar IS ta sanar da daukar alhakin kai harin bom a birnin Alkahira na kasar Masar
2016-12-14 13:30:38 cri
Kungiyar IS ta bada sanarwar ne a daren ranar Talata, inda ta ce ta kai harin bom a wani coci dake birnin Alkahiran kasar Masar a ranar 11 ga wannan wata.

Sanarwar ta bayyana cewa, wani mutum mai suna Abu Abdullah al-Masry ne ya kai harin kunar bakin wake.

A safiyar ranar Lahadi 11 ga wannan watan ne, a kai harin bom a wani coci dake yankin Abassiya na birnin Alkahira na kasar Masar.

Bisa kididdigar da aka yi, harin ya haddasa mutuwar mutane 24, yayin da mutane 49 suka ji rauni. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China