SUNA ya rawaito ministan albarkatun mai da iskar gas na kasar Sudan Mohamed Zayed Awad ya bayyana cewa a jiya Alhamis ya samu sako daga takwaransa na Sudan ta kudu Ezekiel Lol Gatkouth, inda ya bayyana masa cewa rijiyoyin man da aka dakatar da amfani da su a kasarsa za su dawo aiki cikin watanni biyu.
Ya jaddada cewa, an tanadi tsaro 100 bisa 100 don tabbatar da zaman lafiya a jahar ta Unity, ya kara da cewa, harma ya kai ziyarar aiki a inda rijiyoyin man suke a kwanakin baya.
A halin yanzu danyen man da Sudan ta kudun ke samarwa ya ragu da kashi 30 cikin 100, sakamakon barkewar tashin hankali tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan tawaye dake yiwa tsohon shugaban kasar Riek Machar biyayya tun a watan Disambar 2013.
A baya dai kasar tana hako gangar danyen mai 245,000 a kullum, kafin barkewar tashin hankalin, kana daga bisani adadin ya ragu zuwa ganga 160,000 a kowace rana.
Rikicin na Sudan ta kudu yayi sanadiyyar hallaka rayukan dubban jama'a, kana ya tilasta mutane kimanin miliyan 1.9 tserewa daga gidajensu.(Ahmad)