in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon babban magatakardar MDD ya bukaci daukar matakan kandagarkin aukuwar yake yake
2017-01-11 09:41:01 cri
Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bukaci kasashe mambobin majalissar da su sauya manufofinsu, domin cimma nasarar kare aukuwar yake yake a daukacin sassan duniya.

A jawabinsa na farko ga kwamitin tsaron majalissar tun bayan kama aiki, Mr. Guterres ya bayyana bukatar da ake da ita, ta daidaita matakai da ake dauka, ta yadda za a fi ba da karfi ga magance dalilan dake haddasa barkewar rigingimu, da wanzar da zaman lafiya, maimakon daukar matakan warware rikici bayan aukuwar sa.

Guterres ya shaidawa mambobin kwamitin na tsaro su 15 cewa, tuni ya fara daukar wasu matakai na gyaran fuska ga tsarin ayyukan MDD, ta yadda za a rika gano alamun barkewar rikici cikin gaggawa, domin daukar matakan kariya ba tare da bata wani lokaci ba.

Ya ce akwai bukatar tsarin samar da ci gaba na MDDr, ya zamo mai maida hankali ga kandagarki, da bunkasa ayyukan wanzar da zaman lafiya, da samar da ci gaba mai dorewa.

Guterres ya kuma alkawarta inganta amincin dake tsakanin sassan kasashe mambobin MDDr, ta yadda za su ci gajiyar hadin gwiwa a fannin kare aukuwar yake yake. (Saminu Hassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China