Mataimakin wakilin kasar Sin na din-din-din a MDD Wu Haitoa, ya ce babu wata kasa da zata iya samar da cikakken tsaro bisa kashin kanta, ko kuma daga rashin tsaro da wasu kasashe suka fuskanta .
Ya ce dole ne kasashen duniya su dabbaka manufofi da tsare-tsaren MDD ta hanyar hada hannu wuri guda, da nufin samar da wani tsari na tabbatar da tsaro mai dorewa.
Ya kara da cewa, abu ne mai matukar muhimmanci a hada hannu ta hanyar tuntubar juna maimakon yin fito na fito ko mubaya' a, domin mara baya ga muhimmin rawar da MDD da kwamitinta na sulhu ke takawa, wajen magance rikici-rikice da samar da zaman lafiya, da kuma samar da tsarin tabbatar da tsaro da zai karbabbe ga kowa, cike da adalci da gudummuwa da ga kowanne bangare, ta yadda kowa zai amfana.
Har ila yau, Wu ya kuma yi kira da a mai da hankali wajen tabbatar da samun ci gaba ga kowa, domin a cewarsa, zaman lafiya da ci gaba abubuwa ne da suka dogara da juna, inda ya dora alhakin barazanar tsaro da ake samu kamar su yake-yake da rikice-rikice da ayyukan ta'addanci a kan fatara da koma baya. (Fa'iza Mustapha)