Kakakin rundunar sojin Nijeriya ya bayyana a jiya Litinin cewa, sojoji sun gano kaburbura dauke da gawawwakin mayakan kungiyar Boko Haram da suka tsere da raunuka yayin ba-ta-kashin da suka yi da sojojin a farkon watan nan da muke ciki, a yankin arewa maso gabashin kasar.
Cikin wata sanarwar da ya fitar, kakakin rundunar sojin Sani Usman ya ce, dakarun sun gano kaburburan ne lokacin da suke aikin sintiri a yankunan Baga da Kangarwa da Dogonchikun dake jihar Borno, a lokacin da suke farautar 'ya'yan kungiyar Boko Haram da suka tsere.
Sani Usman ya ce, galibin 'yan tada kayar bayan sun mutu ne yayin musayar wuta da aka yi tsakanin su da sojoji a ranar 13 ga watan nan da muke ciki.
A cewarsa, yayin aikin, sojoji sun kuma gano gurnetin hannu a kalla talatin da shida. ( Fa'iza Mustapha)