in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba za a rufe jami'ar Maiduguri saboda harin Boko Haram ba
2017-01-17 09:30:22 cri

Mahukuntan jami'ar Maiduguri da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa, ba za a rufe jami'ar sakamakon harin kunar bakin waken da aka kai wasu sassan jami'ar a jiya da safe ba

Mataimakin shugaban jami'ar Abubakar Njodi wanda ya bayyana wa 'yan jarida hakan a garin na Maiduguri, ya ce, harin ba zai tsorata su har su dauki matakin rufe jamai'ar, yayin da dalibai ke shirin rubuta jarrabawa ba.

A cewarsa, idan aka rufe jami'ar, tamkar bayar da kai ne ga da'awar da 'yan ta'addan ke yi na yaki da ilimin Boko. A don haka ya yi kiran da a kara girke jami'an tsaro a harabar jami'ar don kara tsaurar matakan tsaro.

Jami'in tsare-tsare na hukumar bayar da agajin gaggauwa da ke jihar Borno Satomi Ahmed ya bayyana cewa, kimanin mutane biyar ne harin ya rutsa da su, ciki har da wani farfesa, kana darekta a sashen nazarin ilimin dabbobi na jami'ar. Kuma tuni aka kwashe gawawwakin dalibai hudu da suka mutu sanadiyar harin. A yau Talata ne ake sa ran za a bude jami'ar domin ci gaba da harkokin karatu kamar yadda aka tsara.

Har yanzu dai babu wata kungiya da ta fito fili ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China