Alkaluman tattalin arziki na GDP na Najeriya sun sake yin kasa, sakamakon matsin tattalin arziki da kasar ke fuskanta wanda aka bayyana a hukumance a watan Satumba.
Wasu alkaluma da hukumar kididdiga ta kasar NBS ta fitar a jiya Litinin sun nuna cewa, an samu raguwar GDP na kasar da kashi 2.24 cikin dari a rubu'in uku na shekarar 2016 idan aka kwatanta shi da na makamancin lokacin bara.
Rahoton na NBS ya nuna cewa, cikin watannin da suka gabata danyen man da kasar ke hakowa ya ragu zuwa ganga miliyan 1.63 a ko wace rana, ya yi kasa matuka idan aka kwatanta da na rubu'in biyu na bana.
Najeriya dai ta dogare ne kan albarkatun man fetur a matsayin babbar hanyar samun kudin shigar kasar.
A cewar kididdigar da hukumar ta fitar, an samu karuwar samar da hanyoyin kudin shigar kasar ta fannonin bunkasa aikin gona da harkokin sadarwa, da kuma wasu fannoni da dama.(Ahmad Fagam)