Jami'in rundunar mai kula da yankin Mohammed Garba ya shaidawa manema labarai a garin Warri cewa, an lalata sansanonin tace mai ba bisa ka'ida ba 42, da tan 3,000 na danyen mai da aka sata da tan 1,000 da tataccen man gas a yayin wannan samame.
Jami'in ya kara da cewa, dakarun sun kuma yi nasarar kama wasu jiga-jigan batagarin da ke fasa bututan mai a yankin.
Rundunar sojojin ruwan dai ta lashi takwabin kawar da masu satar mai da sauran munanan ayyukan da ake aikatawa a kan teku.
Rahotanni na nuna cewa, satar mai ta durkusar da kudaden shigar da Najeriyar ta ke samu daga bangaren mai. (Ibrahim).