in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwararru sun yi kira da a inganta harkokin shugabanci a nahiyar Afirka
2016-09-27 10:10:35 cri

Kwararru a harkar tafiyar da harkokin mai daga kasashe 10 na nahiyar Afirka na wani taro a birnin Accran kasar Ghana don tattauna makomar tattalin arzikin nahiyar, a daidai lokacin da ake fuskantar faduwar farashin mai a kasuwannin duniya.

A jawabinsa na bude taron na kwanaki biyu, kana na biyu a jerin taron kolin kula da harkar mai a nahiyar ta Afirka, mataimakin ministan man fetur na kasar Ghana Ben Dagadu, ya yi kira ga kasashen Afirka da su kara fadada kafofinsu na tattalin arziki, domin kaucewa fadawa irin matsalar da aka shiga sakamakon faduwar farashin mai. Ministan ya ce, faduwar farashin man a kasuwannin duniya tilasta wa kasashe rage kasafin kudadensu a bangaren manyan ayyuka.

Shi ma darektan cibiyar tsara manufofi kan makamashi ta Afirka(ACEP) Mohammed Amin Adam, ya bayyana gamsuwa kan yadda wasu kasashe da Allah ya horewa albarkatu ke bullo da wasu matakan sa-ido kan yadda masana'antunsu suke gudanar da ayyukansu, domin sanin irin ci gaba da aka samu a bangaren sarrafa albarkatu.

Taron kolin na wannan shekara zai mayar da hankali kan yadda faduwar farashin mai ta shafi tattalain arziki da ci gaban kasashen Afirka, da kuma yadda harkokin tafiyar da mulki da sauran matakan da aka dauka za su taimaka wajen magance wadannan kalubale.

Taron kolin farko da ya gudana a shekarar da ta gabata, ya yi kira da a karfafa tsarin tafiyar da harkokin mulki ta hanyar daukar matakan shari'a kan yadda ake fitar da mai zuwa kasashen ketare a nahiyar Afirka.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China