Wata sanarwa da kwamitin mai wakilai daga kasashe goma sha biyar ya fitar a jiya Alhamis, ta ruwaito mambobin kwamitin na yin kira ga gwamnatocin kasashen Nijeriya da Kamaru su gudanar da bincike kan al'amarin da nufin hukunta wadanda ke da hannu
A ranar Talata da ta gabata ne, da misalin karfe biyu na rana agogon Nijeriya, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba, suka kai hari kan wani ayarin MDD dake aiki a kusa da iyakar Nijeriya da Kamaru.
Harin ya yi sanadin mutuwar wani dan kwangila na MDD, da 'yan asalin Nijeriya uku da dan kasar Kamaru daya, tare da jikkata wasu daban.
Mambobin kwamitin sun mika sakon ta'aziyya da alhini ga iyalan wadanda suka mutu, da wadanda suka jikkata da gwamnatocin Nijeriya da Kamaru.
Kwamitin ya jadadda bukatar tabbatar da hukunta dukkan wadanda ke da hannu da suka hada da wadanda ke kitsawa, da daukar nauyin ayyukan ta'addanci.
Har ila yau, kwamitin ya nananta cewa, ba za a taba amincewa da duk wani nau'i na ta'addanci daga kowa kuma a ko ina ba, bisa kowane irin dalili. (Fa'iza Mustapha)