Peter Ezemede, shine jami'in hukumar adana jini ta kasar (NBTS) ya tabbatar da hakan ga manema labarai a birnin Benin, na jahar Edo.
Ezemede, ya jadda muhimmancin ayyana bukatar neman gudumowar jinin ne, sakamakon bukatar jinin da ake samun na gaggawa ga mata a lokacin haihuwa, da masu cutar sankarar jini, da kuma mutanen da suka gamu da haddura, wanda a mafi yawan lokutan rashin jinin da za a kara musu ke yin sanadiyyar mutuwarsu.
Jami'in ya bayyana bukatar gaggauta hana dabi'ar cinikin jini a kasar.
Peter, ya bukaci gwamnatocin tarayya da jahohi da kuma daidaikun alummar Najeriyar, dasu bada goyon baya wajen tabbatar da shirin wayar da kan jama'a game bada gudommawar jinin wanda cibiyar ta bullo dashi ya kai ga nasara.