in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin da aka kai a Turkiya
2017-01-02 12:21:33 cri
Kasar Sin ta yi Allah wadai da harin ta'addancin da aka kai a wata mashaya yayin da jama'a ke shagulgulan murnar sabuwar shekara a birnin Istambul na kasar Turkiya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwar, ta ce kasar Sin tana Allah wadai da duk wani nau'i na ta'addanci, kana a shirye take ta hada kai da kasar Turkiya da sauran kasashen duniya a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a duniya.

Jami'ar ta kasar Sin ta kuma bayyana cewa, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya aikewa takwaransa na kasar Turkiya Mevlut Cavusoglu sakon ta'aziya dangane da wannan hari.

Bayanai na nuna cewa, a ranar Lahadi da dare ne wani dan bindiga ya abkawa mashayar Reina, inda ya bude wuta kan daruruwan mutanen da suke shagulgulan sabuwar shekara, inda nan take ya halaka mutane a kalla 39, kana sama da 60 suka jikkata.

Gwamnan birnin Istambul Vasip Sahin ya bayyana harin a matsayin aikin ta'addanci. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China