Rahotannin da shafin internet na ma'aikatar tsaron kasar Rasha ya fitar, sun nuna cewa, Rutskoy ya bayyana cewa, Rasha ta fahimci cewa, yana da wuya a samun nasarar tsagaita bude wuta a kasar Syria, don haka, kasar Rasha tana fatan kasar Amurka za ta sauke nauyin da ke kanta, kana ta yin hadin gwiwa da cibiyar daidaita rikice-rikice da sulhuntawa ta kasar Rasha dake kasar Syria.
Hakazalika kuma, Rutskoy ya ce, tuni cibiyar daidaita rikice-rikice da sulhuntawa ta kasar Rasha dake kasar Syria ta tura rukunin aiki don tabbatar da ganin an tsagaita bude wuta a kasar Syria. (Zainab)