in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rasha za ta rage yawan sojojinta a Siriya
2016-12-30 15:10:40 cri
Jiya Alhamis ne, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya sanar da cewa, kasarsa za ta rage adadin sojojin da ta jibge a kasar Siriya, amma kuma, za ta ci gaba da kokarin yaki da ayyukan ta'addanci a fadin duniya.

Rahoto daga shafin Intanet na shugaban Rasha ya ce, yayin da yake ganawa da ministan tsaro Sergey Shoigu, gami da ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov, Putin ya ce, Rasha za ta ci gaba da yaki da ayyukan ta'addanci ba tare da gindaya wani sharadi ba a duniya, kana za ta kara marawa gwammatin Siriya baya, wajen murkushe ta'addanci, tare da aiwatar da yarjeniyoyin da aka daddale tsakanin kasashen biyu, ciki har da yarjejeniyar girke sojojin Rasha a sansanonin Tartus da Hmeymim dake kasar ta Siriya. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China