in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka na sa ran inganta dangantakar kasar sa da Sin
2017-02-10 10:14:12 cri
A jiya Alhamis, kakakin fadar White House ta kasar Amurka Sean Spicer, ya bayyana a yayin taron maneman labaran da aka saba yi cewa, shugaban kasar Donald Trump, ya amince da muhimmancin dangantakar dake tsakanin kasar sa da Sin, don haka yana sa ran inganta dangantakar sassan biyu.

A daren ranar 8 ga watan nan da muke ciki, fadar White House ta kasar Amurka ta fidda wata sanarwa, inda ta bayyana cewa, shugaban kasar Donald Trump, ya aika wa takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, da jama'ar kasar Sin baki daya sakon murnar bikin Yuanxiao, tare da bayyana fatan raya huldar dake tsakanin kasashen biyu. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China