in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Amurka ya mika sakon murna ga bikin kaddamar da tarukan shawarwari tsakanin Sin da Amurka
2016-06-06 20:14:22 cri
A yau Litinin ne, shugaban kasar Amurka, Barack Obama ya aika da sakon taya murna da fatan alheri ga bikin kaddamar da taron shawarwari kan manyan tsare tsare da tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka karo na 8 da taron musayar ra'ayi tsakanin manyan jami'ai kan al'adu tsakanin kasashen biyu karo na 7.

A cikin sakonsa, shugaba Obama ya bayyana cewa, Amurka da Sin, nasarar da kowacensu ta samu na shafar moriyar juna sosai. Amurka tana maraba da bunkasar kasar Sin mai tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata, tare da fatan ganin babbar gudummawar da Sin za ta bayar a harkokin duniya.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China