Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Mark Toner, ya bayyana a jiya Talata 6 ga wata cewa, ganawar da shugaban kasar Amurka Barack Obama ya yi da takwaransa na kasar Sin Xi Jinping, kafin kaddamar da taron kolin kungiyar G20 wanda ya gudana a birnin Hangzhou na kasar Sin ta haifar da manyan nasarori.
Mr. Toner ya kuma kara da cewa, a cikin 'yan shekarun baya bayan nan, gwamnatin Obama tana kiyaye hadin kai mai karfi a kan wasu lamura. Kana kasarsa tana fatan ci gaba da inganta dangantakar abokantaka a tsakanin ta da kasar Sin.
Bugu da kari, Mr. Toner ya furta a wannan rana cewa, akwai sabani tsakanin kasashen biyu a wasu fannoni, amma duk da haka Amurka ba za ta gujewa sabanin ba, a maimakon haka, za ta ci gaba da tuntubar kasar Sin a kansu. (Kande Gao)