in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kebe kudi Yuan biliyan 1.6 domin kiyaye kayayyakin tarihi na kabilar Tibet daga shekarar 2011 zuwa 2015
2016-07-29 10:44:03 cri

A yayin da ake aiwatar da shiri na 12 na shekaru 5 na raya kasar Sin daga shekarar 2011 zuwa ta 2015, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudi har Yuan biliyan 1.6, domin goyon bayan aikin kiyaye kayayyakin tarihi, da gina dakin nune-nunen kayayyakin tarihi na jihar Tibet, adadin da ya karu da kashi 180 cikin dari bisa lokacin da aka aiwatar da shirin daga shekarar 2006 zuwa ta 2010.

Kawo yanzu dai, yawan kayayyakin tarihin da aka yi musu gyaran fuska ya kai 130, adadin da ya kai matsayin koli a tarihi, wanda ya aza harsashi mai inganci ga aikin nazarin tarihin tudun Tibet, da kuma ba da kariya ga al'adun kabilar Tibet.

Shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin Liu Yuzhu ya furta cewa, a cikin wadannan shekaru 20 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta kebe kudi kusan Yuan biliyan 3, domin aikin kiyaye kayayyakin tarihi na Tibet, da kuma gudanar da ayyuka fiye da 300 irin na gyara da kiyaye su. Daga shekarar 2011 zuwa ta 2015, an kaddamar da aikin gina muhimman wuraren nuna kayayyakin tarihi, da na al'adu na jama'a guda 46 gaba daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China