Hukumar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar yau Jumma'a a shafinta na intanet, ta bayyana cewa,ana saran tattalin arzikin kasar ta Sin zai bunkasa da kimanin kaso 6.7 cikin 100 a shekarar 2016, idan aka kwatanta da hasashen karuwar kaso 2.4 cikin 100 da bankin duniya ya yi kan tattalin arzikin duniya.
A 'yan shekarun nan,kasashen da suka ci gaba, kamar wadanda ke cikin kungiyar tarayyar Turai da Amurka da Japan, ba su taka wata gagarumar rawa ga bunkasar tattalin arzikin duniya ba.
Sannan kuma kasashe kamar Brazil da Rasha ba su fita daga matsalar tattalin azrikin ba. Haka kuma duk da saurin ci gaban tattalin arzikinta, kasar Indiya ba ta zama kashin bayan ci gaban tattalin azrikin duniya ba, saboda karancin ci gaban tattalin arzikinta.
Bayanin na nuna cewa, sabbin matakan da kasar Sin ta dauka na raya tattalin arzikinta, sun taimaka mata wajen canjawa daga tattalin arzikin da ya dogara ga fitar da kayayyaki da zuba jari, zuwa tsarin tattalin arziki mai dorewa wanda ya ke kara samar da kayayyaki, hidima da kuma kirkire-kirkire.
Duk da raguwar saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar a 'yan shekarun nan, har yanzu shi ne mafi saurin bunkasa a duniya.(Ibrahim)