A jiya Alhamis ne wani masanin harkokin tattalin arziki ya ce, ana sa ran a samu kimanin tafiye-tafiye biliyan 2.98 yayin bikin bazara na bana a kasar Sin, tsakanin yau 13 ga wata da 21 ga watan Fabreru.
Yayin wani taron manema labarai, kakakin hukumar rayawa da sake fasalin kasar, Zhao Chenxin ya ce idan aka kwatanta da na bara, adadin ya karu da kashi 2.2, inda aka fi samun yawan tafiye-tafiyen ta jirgin sama, a matsayinsa na wanda ya fi sauran fannonin sufuri sauri.
Zhao ya kara da cewa, hukumomin kula da sufuri sun shirya tsaf domin tunkarar tafiye-tafiyen, sai dai hazo da dusar kankara da sauran matsalolin yanayi a wasu yankunan, ka iya kawo matsala ga tafiye-tafiyen a bana.
Bikin na bazara a wannan shekarar zai gudana ne a ranar 28 ga wannan watan na Junairu da muke ciki.
Bikin dai, na taka muhimmiyar rawa wajen sada iyalai.( Fa'iza Mustapha)