in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta ba kamfanonin kasashen waje karin damarmaki
2017-02-08 09:39:33 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya ce kasar Sin ta kuduri aniyar ba kasashen waje karin damarmaki ta yadda kamfanonin za su rika zuba jari a kasar.

Lu kang, wanda ya bayyana haka lokacin da yake zantawa da manema labarai, ya ce kasar Sin za ta samar da kyakkyawan yanayin zuba jari ga kamfanonin kasashen waje.

A nata bangare, Kwamishinar harkokin cinikayya ta tarayyar Turai, Cecilia Malmstorm, ta ce ta amince da furucin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi yayin babban taro kan tattalin arziki na duniya da ya gudana a Davos cikin watan da ya gabata, inda ya ce babu wanda zai yi nasara idan har kasashe na kakabawa juna matakan cinikayya masu tsauri.

Ta ce babban kalubalen dake gaban kasar Sin a bana shi ne, samar da gyare-gyare da za su yi daidai da furucin na shugaban kasar.

A cewar Lu Kang, a ko da yaushe, kasar Sin na mutuntawa tare da saukaka batutuwan da suka shafi cinikayya da zuba jari, inda kuma kasar ke adawa da duk wani nau'i na sanya matakan cinikayya masu tsauri. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China