A bana cinikayyar da aka yi a ranar 11 ga watan 11n nan, ta nuna irin ci gaba da manyan kamfanonin cinikayyar yanar gizo kamar su Vipshop, da JD da Alibaba suka samu.
Alkaluma sun nuna cewa, darajar kudaden cinikayya da kamfanoni suka samu ta wannan hanya ya karu daga Yuan miliyan 52 a shelarar 2009, zuwa Yuan biliyan 91.2 a bara. Sai da kuma a hannu guda masu kasuwanci bisa tsari na al'ada da aka saba da shi a kasuwanni, na fuskantar koma baya a nasu bangaren cinikayyar.