in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: babu wata kasa daya tilo dake da ikon tabbatar da ka'idojin cinikayyar duniya
2016-05-03 19:51:59 cri
A Talatar nan ne ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta mayar da martani ga ra'yin kasar Amurka game da yarjejeniyar tattalin arziki ta TPP da ta RCEP, inda kakakin ma'aikatar Hong Lei, ya bayyana cewa kamata ya yi kasashe daban daban su yi shawarwari da juna game da ka'idojin cinikayyar duniya, tare kuma da tsaida kuduri kan su, amma ba wata kasa daya tilo ta yanke hukunci kan hakan ba.

A kwanakin baya ne dai shugaban kasar Amurka Barack Obama, ya gabatar da wani sharhi dake cewa, yanzu haka kasar Sin da wasu kasashe na zantawa kan yarjejeniyar RECP. Kuma yarjejeniyar TPP da aka cimma matsaya kan ta karkashin jagorancin Amurka tana bin babban ma'auni na hada-hadar cinikayya, wanda hakan ya ba da tabbacin cewa, Amurkan ce za ta tsara ka'idojin cinikayyar duniya na karni 21, maimakon sauran kasashen duniya ciki har da kasar Sin.

A yayin taron manema labaru da aka shirya a Talatar nan, mista Hong Lei ya amsa tambaya kan wannan ra'ayin na shugaba Obama, yana mai cewa Amurka na daukar babban matsayi kan wannan batu, amma ba ta da damar yin hakan bisa doka. {Bilkisu}

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China