in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta kare 'yancinta kamar yadda ya kamata domin kare tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban
2016-12-12 20:30:15 cri
A yau Litinin, 12 ga wata, Mr. Gao Hucheng, ministan kasuwancin kasar Sin ya bayyana cewa, dakatar da zaben da aka shirya gudanarwa a wata kasa a lokacin da ake binciken matsalar cinikayya game da kasar Sin, nauyin ne da ke kan kasashen duniya kamar yadda dokokin kasa da kasa suka tanada. Muddin wasu kasashe ba za su sauke hakikanin nauyin da ke kansu ba, ko shakka babu, kasar Sin za ta tsaya kan matsayinta na kare 'yancinta na yin ciniki, kana za ta hada kai da sauran mambobin kungiyar WTO, ta yadda za ta yi amfani da 'yancinta na kara daukar matakan kare tsarin yin cinikayya tsakanin bangarori daban daban kamar yadda ake fata.

Kamar yadda doka ta 15 game da yarjejeniyar shigar kasar Sin cikin kungiyar WTO ya nuna a shekaru 15 da suka gabata, a cikin farkon shekaru 15 da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, a lokacin da ake binciken matsalolin farashin kayan da suka fito daga kasar Sin, ana iya zabar farashin kayan wata kasa daban domin tabbatar da ganin ko kasar Sin ta karya farashin kayanta fiye da kima. Amma bayan shekaru 15, wato tun daga jiya Lahadi, 11 ga watan Disamban shekarar 2016, aka dakatar da amfani da wannan hanya. Amma har yanzu kasar Amurka da kawancen kasashen Turai, wato EU ba su sauke wannan nauyin da aka dora musu kamar yadda ya kamata ba. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China