in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tattaunawa kan zuba jari da cinikayya na kasa da kasa karo na 19 a kasar Sin
2016-09-09 12:32:12 cri

A jiya ne aka bude taron tattaunawa kan harkokin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa karo na 19 kuma dandalin zuba jari na kasa da kasa na shekarar 2016 a birnin Xiamen dake gabashin kasar Sin, kuma mataimakin firaministan kasar Sin Mista Wang Yang ya halarci taron tare da ba da jawabi, inda ya nanata cewa, ya kamata a yi amfani da wannan taro don bunkasa harkokin zuba jari da hadin gwiwa da kara habaka fannonin da ake bude kofa ga kasashen waje da kyautata halin da kamfanonin masu jarin kasashen waje ke ciki, da kuma sa kaimi ga bullo da sabon tsarin tattalin arziki na tsarin bude kofa bisa jigon taron wato "Kirkire-kirkire, Daidaitawa, Kiyaye muhalli, Bude kofa" da kuma matsaya daya da aka samu a gun taron G20 da aka yi a birnin Hangzhou.

Mista Wang Yang kuma ya kara da cewa, tun kasar Sin ta dauki manufar yin kwaskwarima da bude kofa ga kasashen waje, Sin tana nacewa ga hanyar shigo da jarin kasashen waje da kuma zuba jari ga kasashen waje, wadda ta kai matsayin farko tsakanin kasashe masu tasowa ta fuskar shigo da jarin kasashen waje a cikin shekaru 24 a jere, kuma tana sahon gaba a duniya a cikin shekaru biyar a jere a fannin zuba jari a kasashen waje, matakin da ya tabbatar da matsayinta na kasa mafi karfi wajen shigo da jari daga kasashen waje da kuma zuba jari a kasashen waje. Don haka, Sin za ta ci gaba da daidaita manufofinta na shigo da jarin kasashen waje, da kyautata tsarin bude kofa ga kasashen waje, ta yadda za a samar da wani hali mai daidaito, adalci da kuma karko. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China