Ya ce mahukuntan kasar na daukar matakai daban daban na cimma wannan kuduri, ciki hadda yiwa matatun man kasar mallakar gwamnati garan bawul. A daya hannun kuma, matatar mai da dan kasuwar nan Aliko Dan Gote zai gina a kasar, ita ma za ta bunkasa yawan tacaccen man da kasar ka iya samarwa da zarar an kammala aikin ta.
Yanzu haka dai a cewar ministan, matatun man kasar na samar da litoci miliyan 8, cikin lita miliyan 20 ta man fetur da ake amfani da shi a kullum.
Najeriya dai na fatan nan da shekarar ta 2019, za ta iya samar da isasshen man fetur da take bukata a cikin gida, kana za ta daina musayar danyen mai da wasu kamfanonin kasashen ketare da nufin samun tacaccen man. (Saminu Hassan)