Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wani kwamiti da nufin aiwatar da matakan kasar na tsaron harkokin Intanet.
Babban darektan hukumar ta NITDA Isa Patanmi shi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa wannan mataki zai kawo karshen barazanar kutse da harkokin Intanet ke fuskanta a kasar.
Isa Pantami ya kara da cewa, manufar kafa wannan kwamiti sun hada da ilimantar da al'ummar Najeriya game da bukatar da ake da ita ta magance barazanar kutse da harkar intanet ke ciki, amfani da masana a wannan fanni da sauransu.
Ana sa ran kwamitin ya tsara tare da yin musayar muhimman bayanai da amfani da sabbin dabarun tsaron Intanet. Sun dai mambobin kwamitin an tsamo su ne daga ma'aikatar sadarwa ta kasar, da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, da hukumar ta NITDA, da hukumar aikewa da wasiku, da hukumar kula da harkokin kwamfuta da tauraron dan-Adam ta Najeriya da sauransu.
Alkaluman na nuna cewa, daga cikin 'yan Najeriya kimanin miliyan 97 masu sha'awar amfani da Intanet, kimanin kaso 14 cikin 100 ne ke fuskantar barazanar kutse. Wannan a cewar hukumar yana daga cikin dalilan da suka tilasta mata kafa wannan kwamiti.(Ibrahim)