Harin na jiya Labara dai ya auku ne lokacin da 'yan tawagar kwararru dake sanya ido kan wasu ayyukan musamman na majalissar, ke hanyar kauyen Hosere Jongbi, daura da Kontcha.
Da yake karin haske game da lamarin, kakakin MDDr Stephane Dujarric, ya ce tawagar na aiwatar da wani shiri ne da ya shafi yunkurin da ake yi, na kawo karshen takaddama kan wasu yankuna na iyakar kasashen Najeriya da Kamaru mai lakabin CNMC.
An dai kafa shirin CNMC bisa umarnin babbar kotun kasa da kasa, a wani mataki na samar da daidaito da tsaro a yankin.
Rahotanni sun nuna cewa kawo yanzu ba a tantance ko su wane ne suka kaddamar da wannan harin ba. (Saminu)