Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa, shugaban kasar Muhammadu Buhari ya tsawaita lokacin dawowarsa daga hutun da ya ke yi ne bisa shawarar da likitoci suka ba shi na kammala wasu binciken lafiya.
Mai baiwa shugaban shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Femi Adesina, wanda ya bayyana hakan yayin wata hira da gidan talabijin na kasa NTA a jiya Lahadi, ya ce duk da hutun da shugaban ya ke a birnin London, mataimakinsa yana tafiyar da harkokin mulki kamar yadda kundin tsarin mlkin kasar ya tanada.
A cewarsa, karin hutun da shugaban ya yi, zai ba shi damar hutuwa kafin ya dawo gida.(Ibrahim)