in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An shirya biki a kwalejin Confucius dake jami'ar Legas
2017-02-07 20:04:29 cri

A jiya Litinin ne, aka shirya bikin murnar bikin bazara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin a kwalejin Confucius dake jami'ar Legas a Najeriya, bikin da ya samu halartar karamin jakadan kasar Sin a jihar Legas Chao Xiaoliang, da mataimakin shugaban jami'ar Legas shehu malami Duro Oni, gami da wakilan wasu kamfanonin kasar Sin.

Cikin wadanda suka nuna fasahohi a yayin biki akwai daliban kwalejin Confucius, gami da wasu daliban makarantun firamare da sakandare fiye da 400. Inda suka rera wakoki, da raye-raye, da fasahar kare kai ta gargajiyar kasar Sin wato Kunfu, da dai sauransu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China