Babban hafsan tsaron kasar Gabriel Olonisakin, shi ne ya tabbatar da hakan a Abuja, ya kara da cewa, ba za su taba yin kasa a gwiwa ba wajen magance duk wani abu da ka iya yin barazana ga zaman lafiyar kasar.
A jawabin da ya gabatar ya bayyana cewa, dakarun Najeriya suna zaune cikin shirin kota-kwana a koda yasuhe.
Olonisakin ya kuma yi alkawarin cewa sojojin Najeriya za su bullo da wani shiri na tsaron dazuka domin bankado duk wasu bata gari dake samun mafaka a irin wadannan wurare.
Jami'in ya yabawa sojojin kasar wajen kokarinsu da suke ci gaba da yi na dakile rikicin 'yan tada kayar baya a shiyyar arewa maso gabashin kasar da yankin Niger Delta da ma sauran sassan kasar. (Ahmad Fagam)