Cikin wani sako da kamfanin dillancin labarai na kasar Sin Xinhua ya samu game da aukuwar lamarin, hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya NEMA, ta ce dan kunar bakin waken yaro ne dan kusan shekaru 10, ya kuma yi yunkurin kutsa kai cikin masallacin ne, lokacin da wani matashi ya dakatar da shi, nan take kuma ya tada Bam din dake jikin sa, wanda hakan ya hallaka shi tare da matashin da ya bincike shi.
Wannan hari wanda ake dangantawa da kungiyar Boko Haram, na zuwa ne 'yan kwanaki, bayan da wasu 'yan kunar bakin waken suka kaiwa jami'ar Maiduguri hari.
Ana dai hasashen cewa mayakan kungiyar ta Boko Haram na sake haduwa ne a sassan birnin na Maiduguri, bayan da sojojin kasar suka ce sun fatattake su daga dajin Sambisa.
Daga shekarar 2009 kawo wannan lokaci, kimanin mutane 20,000 ne suka rasa rayukan su, baya ga wasu sama da miliyan 2 da dubu dari 3 da suka rasa matsugunan su, sakamakon ayyukan kungiyar.
Kungiyar dai ta sha daukar alhakin hare haren dake aukuwa a sassan yankin arewa maso gabashin Najeriya. (Saminu)