Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da ministan tsaron kasar Avigdor Lieberman, sun amince da gina karin matsugunan yahudawa 2,500, a yankunan gabar yammacin kogin Jordan, inda yahudawa ke ci gaba da yin kaka gida.
Wata yarjejeniyar da firaministan da ministan suka sanyawa hannu, ta fayyace tsarin gine ginen, tana mai cewa za a yi su ne da nufin amsa bukatun muhalli na al'ummar yahudawa.
Jami'an biyu, sun kuma ce yanzu rayuwar yahudawa za ta inganta, a wani furuci mai kama da shagube ga manufar tsohon shugaban Amurka Barack Obama, wanda ya sha sukar gina matsugunan yahudawan a yankunan Falasdinu.
A ranar Lahadin da ta gabata ma dai Netanyahu, ya shaidawa majalissar ministocin sa cewa, ya amince da ci gaba da ginin matsugunan yahudawa a gabashin birnin Jerusalem.
Kalaman na Mr. Netanyahu dai na zuwa ne bayan da hukumar birnin Jerusalem mai kula da tsarin gine gine, ta amince da gina sababbin gidaje 560 a yankunan Ramot, da Ramat Shlomo, da kuma Pisgat Ze'ev, a wani yanki dake Isra'ila da ta hade da birnin Jerusalem, duk kuwa da rashin amincewa da sassan kasa da kasa suka nuna ga hakan.
Isra'ila ta kwace gabashin Jerusalem ne tun a shekara 1967, tare da sauran yankunan yammacin kogin Jordan, da zirin Gaza. Daga bisani kuma ta hade su da gabashin Jerusalem, tana mai ayyana shi a matsayin fadar mulkinta ta cikin gida, duk kuwa da suka da hakan ke sha daga kasashen duniya.