in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kamaru ta lashe kofin AFCON
2017-02-06 19:47:27 cri


A jiya Lahadi ne, kasar Kamaru ta doke kasar Masar da ci biyu da daya a wasan karshe na gasar cin kofin AFCON da aka gudanar a kasar Gabon, wannan ya baiwa kasar ta Kamaru sake lashe kofin AFCON tun bayan da ta ci kofin a shekarar 2002.

Kasar Masar ce ta fara zura kwallo a minti na 22 na farkon rabin lokaci ta hannun dan wasanta Mohammed Elneny wanda ya ke buguwa kulob din Arsenal ta kasar Ingila wasa.

Bayan an dawo daga hutun rabin lokaci ne, kasar Kamaru ta farke kwallon ta hannun dan wasanta Nkoulou, wannan ya sa kungiyoyin biyu suka yi kunnen doki. A minti na 89, dan wasan kasar Kamaru Aboubakar ya kara zura kwallo a ragar Masar, wanda hakan ya baiwa Kamaru nasarar doke Masar da ci biyu da daya, abin da ya ba ta nasarar lashe kofin AFCON a wannan karo.

Da wannan nasara Kamaru ta sake cin kofin AFCON bayan shekaru 15, wannan shi ne karo na 5 da Kamaru ta lashe kofin a tarihi. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China