A watan Oktoban da ya gabata ne, jaridar "The Huffington" ta kasar Amurka ta wallafa wani labarin da ke cewa, kasar Iran za ta tura sojojinta zuwa kasar Iraki domin 'yantar da birnin Mosul. Game da labarin, Mr. Ali Akbar Velayati, mai ba da shawara ga shugaban koli na Iran, kana tsohon ministan harkokin wajen kasar Iran ya taba bayyana a ran 19 ga watan Oktoba, cewar kasar Iran ba za ta tura sojojinta zuwa kasar Iraki domin 'yantar da birnin Mosul da ke hannun IS, amma ta ba da wasu shawarwarin soja kawai kamar yadda gwamnatin kasar Iraki ta bukata. (Sanusi Chen)