Dandalin bunkasa sana'o'in Sin da Afirka zai taimakawa kanana da matsakaitan kamfanonin Sin su shiga nahiyar Afirka
A jiya ne aka kaddamar da aikin kafa dandalin sa kaimi ga bunkasuwar sana'o'in Sin da Afirka na farko a yankin fitar da kayayyaki dake birnin Nairobi na kasar Kenya. Ana sa ran bayan da kaddamar da wannan dandali, za a samar da hanyoyin da suka dace ga kanana da matsakaita kamfanonin Sin ta yadda za su shiga kasuwar nahiyar Afirka.
A jawabinsa yayin kaddamar da shirin ministan kula da masana'antu da raya kamfanoni na kasar Kenya Adan Mohammed ya bayyana cewa, dandalin zai samar da kyakkyawar yanayin da ya dace ga kanana da matsakaita kamfanonin Sin su shiga kasar Kenya tare da taimakawa wajen kara hadin gwiwa a tsakanin kamfanonin Sin da Afirka. (Zainab)