in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron tattaunawa kan hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da Afirka karo na 6
2016-11-23 12:41:41 cri
An bude taron kara wa juna sani kan hadin gwiwar kiwon lafiya a tsakanin Sin da Afirka karo na 6 a birnin Shanghai na kasar Sin a jiya Talata, inda aka dora muhimmanci ga ingancin magani.

Shugabar hukumar kula da kiwon lafiya da kayyade iyali ta kasar Sin Li Bin, ta bayyana cewa, Afirka tana da albarkatun halittu da kwadago, kana tana cikin wani mataki na bunkasa masana'antu. A cikin shekaru fiye da 30 da Sin ta aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, yawancin magungunan da Sin ta samar suna da ingancin da ya kai ma'aunin duniya. Ana bukatar juna a tsakanin Sin da Afirka a fannin hadin gwiwar samar da magani, kana suna fuskantar kyakkyawar dama a yanzu. A nan gaba, Sin za ta ci gaba da nuna goyon baya ga kamfanonin samar da magani na kasar da su shiga kasashen Afirka, da sa kaimi ga kamfanoni da jami'o'i da kungiyoyi da mutane masu zaman kansu da su shiga wannan aiki don gaggauta samar da fasahohi da magani a kasashen Afirka, ta haka ne za a samar da magani mai inganci da araha ga jama'ar kasashen Afirka. Kana tana fatan kasashen Afirka za su samar da saukin ciniki da tsara manufofin sa kaimi ga kamfanonin Sin da Afirka da su hada kai, ta haka za a amfanawa jama'ar Afirka ta hanyar samar musu magani mai inganci, kana tana maraba da kamfanonin Afirka da su zo kasar Sin don zuba jari a fannin kiwon lafiya da likitanci. Haka zalika, tana fatan kungiyoyin duniya ciki har da hukumar kiwon lafiya ta duniya da su ci gaba da nuna goyon baya ga ingancin maganin Sin, da sa kaimi ga maganin Sin mai inganci da araba da su shiga nahiyar Afirka.

Shugaban gudanarwa na asusun kula da yawan mutane na MDD wato UNFPA Babatunde Osotimehin yana ganin cewa, bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, musamman bayan da Sin ta bude kofa ga kasashen waje da yin kwaskwarima a gida, ana samun babban ci gaba a fannin kiwon lafiya a kasar Sin, kuma ya kamata kasashen Afirka su koyi fasahohinta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China