Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, zai fara ziyarar aiki ta farko a wannan shekara a kasashen Madagascar, Zambiya, Tanzaniya, Congo da Nijeriya, tsakanin ranekun 7 zuwa 12 ga wata.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, shi ne ya fadi hakan a yau Talata 3 ga wata a nan Beijing, inda ya kara da cewa, manufa mafi muhimanci da mista Wang yake fatan cimmawa a wannan karo ita ce, a yayin da ake tinkarar sabbin sauye-sauye a harkokin siyasa da tattalin arziki a duniya, kana kasashen Afirka ke fuskantar sabon kalubale ta fuskar bunkasuwa, ya ingiza manufar kasar Sin ta amfani da wannan zarafi, wajen zurfafa mu'amala da kasashe masu ruwa da tsaki, dangane da yadda za a aiwatar da ra'ayi daya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin da takwarorinsa na kasashen Afirka suka cimma, da kuma sakamako da aka samu a yayin taron dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka na Johannesburg, a kokarin farfado da nahiyar Afirka, da sabunta hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka, da ba da gudummowa wajen inganta hadin kan kasashe maso tasowa, da kuma samun bunkasuwa tare. (Tasallah Yuan)