in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu shugabannin kasashen Afirka sun taya Sinawa murnar bikin bazara
2017-01-28 13:30:19 cri
Gabannin bikin bazara na 'shekara ta zakara' bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, wasu shugabannin kasashen Afirka sun mika sakwanni don taya daukacin al'ummar kasar murnar shiga sabuwar shekara.

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da nasa sako ta shafin sada zumunta, inda ya taya daukacin al'ummar kasar Sin murnar shiga sabuwar shekara ta zakara. Buharin ya ce, bikin bazara, kasaitaccen biki ne ga dukkan Sinawa, wadanda kamata ya yi su koma garinsu don haduwa da iyalansu.

Hakan na nufin cewa, mutanen Sin da na Najeriya na da ra'ayoyi masu kama da juna, wato mayar da hankali sosai kan iyali.

Muhammadu Buhari ya kara da cewa, kasar Sin babbar aminiya ce da Najeriya ke son hada-gwiwa da ita, don haka yana fatan a sabuwar shekara ta zakara ta kasar Sin, hadin-gwiwar kasashen biyu za ta kara samun nasarori da dama.

A nasa bangaren, shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma ya gabatar da sakon taya murna ta shafinsa na yanar gizo, inda a madadin gwamnati gami da jama'ar kasar Afirka ta Kudu, ya godewa Sinawa mazauna kasar saboda gudummawar da suka bayar ga ci gaban tattalin arziki da rayuwar al'ummar kasar, inda ya kuma mika fatan alheri da sahihiyar gaisuwa ga dukkanin Sinawa.

Zuma yana kuma fatan Sin da Afirka ta Kudu za su karfafa hadin-gwiwa, da sanya sabon kuzari wajen raya dangantakarsu ta gargajiya, ta yadda za a samar da zaman wadata ga al'ummar kasashen biyu. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China