in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hutun bikin bazara na Sinawa ya zamo wata babbar dama ga sashen bude ido
2017-01-28 13:18:04 cri
Hukumar kasar Sin mai kula da harkokin yawon shakatawa, ta bayyana hutun mako guda na bikin bazara da Sinawa ke gudanarwa a farkon kalandar gargajiya a kowace shekara, a matsayin wata dama ta samun kudaden shiga ga bangaren harkar yawon shakatawa.

Hukumar ta ce bikin bazara na bada dama ga al'ummar Sinawa su hadu da iyalai da 'yan uwa, amma a halin yanzu Sinawa da dama kan yi amfani da hutun nasu wajen ziyartar kasashen ketare. Hukumar ta ce a bana kimanin Sinawa miliyan 6 ne ke gudanar da hutun na bikin bazara a kasashen ketare.

Shi ma kamfanin shirya tafiye tafiye na Ctrip, ya bayyana kan shafinsa na yanar gizo cewa, yayi hasashen Sinawa 'yan yawon bude ido, za su kashe kudade da suka kai kusan dalar Amurka biliyan 14.5 cikin makon na hutu, yayin da suke tafiye tafiye.

Ctrip ya ce Sinawa na kara yawan kudi da suke kashewa wajen tafiye tafiye, sakamakon karuwar kudaden shiga da suke samu, da saukaka matakan samun Visa ta kasashen waje, da kuma karuwar jirage dake sufurin fasinjoji.

Kasar Sin dai ita ce ke kan gaba cikin shekaru 4 a jere, a yawan 'yan kasar dake fita yawon bude ido kasashen ketare.

'Yan kasar na kashe kaso 13 bisa dari na daukacin kudade da ake kashewa, a yawon shakatawa tsakanin kasashen duniya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China