in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Al'ummar Sinawa na shirin bikin Bazara
2017-01-27 12:44:07 cri

Shugabannin kasashen duniya na ci gaba da mika sakon fatan alheri ga daukacin Sinawa, yayin da suke shirin fara bikin Bazara, biki mai muhimmancin ga daukacin iyalan Sinawa dake sassan daban-daban na duniya.

A sakonsu na fatan alheri ga Sinawa game da wannan biki, wasu daga cikin shugabanin kasashen duniya suna fatan karfafa dangantakar abokantaka da kasar Sin

A sakonta na fatan alheri da ta aike ta shafin intanet na gwamnatin, Firaministar Burtaniya Theresa May ta yi alkawarin kara bunkasa hadin gwiwar da ke tsakanin Burtaniya da kasar Sin.

Shi ma shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana tabbaci game da bunkasar hadin gwiwar Sin da Najeriya bisa manyan tsare-tsare. Yana mai cewa,kasashen biyu sun cimma yarjejeniyar samun moriyar juna a fannin tattalin tattalin arziki da sauran fannoni.

Shugaba Buhari ya bayyana a cikin wata sanarwa da ofishin ya rabawa manema labarai cewa,bikin bazara na al'ummar Sinawa ya kara jaddada muhimmancin haduwar iyali, al'adar da Najeriyar ma ke mutuntawa.

A lokacin wannan biki dai ofisoshin jakadncin kasar Sin da daukacin Sinawa a sassa daban-daban na duniya kan shirya shagulgula don yi mu'amala da 'yan uwa da abokan arziki.

Za a yi bikin bazara na bana ne a ranar 28 ga wannan wata da muke ciki.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China