Bisa wannan kudurin, adadin sojojin tabbatar da zaman lafiya na MDD ya kai dubu 10 da 750, tare da 'yan sanda 2080, kuma za su ci gaba da aikin sintiri. Muhimmin nauyin da aka dorawa rundunar shi ne, kiyaye fararen hula, da kare hakkin bil Adama, da samar da yanayin tsaro don aikin jigilar kayayyakin jin kai a kasar Afirka ta tsakiya.
Wannan kuduri ya kuma bayyana cewa, kwamitin sulhu na MDD yana maraba da Faustin-Archange Touadera da ya hau kan mukamin shugabantar kasar, da kuma kafa sabuwar gwamnatin kasar. Sannan ya nemi gwamnatin Afirka ta tsakiyar ta hanzarta samar da daidaito tsakaninta da bangarori daban daban na kasar, kuma ta girmama tsarin mulkin kasar da tabbatar da samun dauwamammen ci gaban kasar cikin lumana. (Sanusi Chen)