in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojin Nijeria za ta bada ladan kudin ga duk wanda ya taimaka mata da bayanai kan 'yan kunar bakin wake
2017-01-18 09:56:34 cri
A jiya Talata ne hukumomin rundunar sojin Nijeriya suka sanar da ba da ladan Naira dubu dari biyar, kwatankwacin dalar Amurka dubu daya da dari shida, ga duk wanda ya taimaka da bayanai da za su kai ga kama 'yan kunar bakin wake, ko gano inda ake hada bama-bamai.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a Lagos, kakakin rundunar sojin, Birgediya Janar Sani Usman Kuka-Sheka, ya ce an dauki matakin ba da ladan ne la'akari da yadda ake samun yawaitar hare-haren kunar bakin wake a yankin arewa maso gabashin kasar, musammam birnin Maiduguri da garin Madagali, da a nan hare-hare suka fi ta'azzara.

Ya ce matakin na rundunar sojin, zai kara karfafawa al'ummar kasa masu kishin kasa, shiga a dama da su wajen yakar ta'addanci tare da wanzar da tsaro. ( Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China