Daya daga 'yan kunar bakin waken dai ta hallaka kan ta, tare da wani dake kusa da wurin da ta tashi bam din dake jikinta, kana wasu mutanen 4 suka jikkata.
A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno Damian Chukwu, tsakanin tsakar daren ranar Talata zuwa safiyar Laraba, an samu yunkuri na kunar bakin wake har karo 3, a birnin Maiduguri fadar mulkin jihar Borno, wadanda dukkanin su 'yan kunar bakin waken suka tarwatsa kan su bayan da aka gano nufin su.
Mr. Chukwu ya ce bam na farko ya tarwatse ne a daren Talata, lokacin da dan kunar bakin waken dake tare da shi, ya yi kokarin kutsawa cikin birnin na Maiduguri ta wani kauye, kuma wasu jami'an soji suka harbe shi da bindiga.
Sai kuma Bam na biyu wanda ya tashi yayin da mai dauke da shi, ke kokarin shiga birnin ta iyakar kauyen Kaleri a ranar Laraba. Yayin da kuma na uku, wata mata ta tada shi, yayin da take kokarin gujewa jami'an tsaro a wannan yanki.
Mr. Chukwu ya ce tuni aka garzaya da wadanda suka jikkata sakamakon aukuwar wannan lamari zuwa asibiti. (Saminu)