in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyar Boko Haram ta dauki nauyin harin da aka kai Jami'ar Maiduguri
2017-01-18 09:37:03 cri
Kungiyar 'yan tada kayar baya ta Boko Haram, ta dauki nauyin harin kunar bakin wake da aka kai da sanyin safiyar Litinin a Jami'ar Maidugurin jihar Borno, dake yankin arewa maso gabashin Nijeriya.

'Yan sandan garin sun ce harin kunar bakin wake da mutane biyu suka kai ciki har da yaro dan shekaru bakwai, ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane biyar tare da raunata wasu goma sha biyar.

Da yake jawabi cikin wani faifan bidiyo da harshen Larabci, wani da ya yi ikirarin shi ne Abubakar Shekau, ya ce sun kai hari masallacin cikin jami'ar ne domin sun dauke shi matsayin wanda ake aikata sabo cikinsa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China