Da sanyin safiyar Litinin din nan ne wasu 'yan kunar bakin wake suka kaiwa jami'ar Maiduguri dake jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya harin Bam, lamarin da ya sabbaba rasuwar mutane 5, tare da jikkatar wasu karin mutanen 15.
A cewar kwamishinan 'yan sandan jihar ta Borno Damian Chukwu, wani yaro ne dan shekaru kusan 7 ya tada Bam din dake jikin sa, a wani masallaci dake rukunin gidajen manyan ma'aikatan jami'ar, nan take kuma ya hallaka kan sa da sauran mutanen da lamarin ya rutsa da su.
Gabanin hakan kuwa, wani jami'in tsaro ya harbe daya daga 'yan kunar bakin waken, lokacin da yake yunkurin tsallaka daya daga kofofin jami'ar, nan take kuma Bam din dake jikin sa ya tarwatse.
Da yake karin haske game da halin da ake ciki, jami'in tsare tsare na hukumar bada agajin gaggawa a jihar ta Borno Satomi Ahmed, ya ce wani shehun malami dake aiki a sashen kula da lafiyar dabbobi a jami'ar, na ciki mutane 5 din da suka rasa rayuwar su yayin wannan lamari, baya ga wasu dalibai su 4. Ya ce yanzu haka ana ci gaba da aikin ceton rayuwan sauran wadanda suka jikkata sakamakon harin.(Saminu Alhassan)