in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Matakin Trump na hana 'yan gudun hijira shiga Amurka ya haifar da bore a gaban White House
2017-01-30 12:58:38 cri

Rahotanni daga Amurka na cewa, dubban masu zanga-zanga ne suka taru a gaban fadar White house a jiya Lahadi don yin Allah wadai da matakin shugaba Trump na hana dukkanin 'yan gudun hijira da ma 'yan kasashe bakwai da ke yankin gabas ta tsakiya da na arewacin Afirka shiga Amurka.

Bugu da kari wasu masu zanga-zangar sun yi dafifi a filayen jiragen saman kasar fiye da 30 don nuna rashin jin dadinsu da wannan mataki.

Jami'a a fadar ta White House Kellyanme Conway ta bayyana cewa, wannan haramci da Amurkan ta dauka ya karfafa tsaron kasar duk da cewa ya kawo tsaiko ga harkokin sufurin kasa da kasa.

A daya hannun kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawan Amurka Chuck Schumer ya bayyana a jiya Lahadi cewa,'yan jam'iyyar democrat na duba yiwuwar daukar matakan doka don ganin an soke wannan haramci

A ranar Asabar ce wani alkalin tarayyar Amurka ya bayar da umarnin gaggawa na hana kora ko tsare bakin da suka shigo kasar wadanda a halin suke da takardar iznin zama ko suka gabatar da bukatar neman takardun iznin zama a cikin kasar, biyo bayan dokar da Trump din ya sanyawa hannu.

Bugu da kari, kotu ta yanke irin wannan hukunci a jihohin Virginia,Massachusetts da Washington.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China