in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashe da kungiyoyi sun yi Allah wadai da matakin Trump na hana musulmi shiga kasar Amurka
2017-01-30 12:47:38 cri
Kasashe da yankuna na ci gaba da yin tofin Allah tsine game da matakin baya-bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya dauka na hana musulmi daga kasashe bakawi shiga kasar ta Amurka.

Wadannan kasashe da haramcin ya shafa wato Syria,Iraki,Yemen,Libya,Somaliya, Sudan da Iran sun yi Allah wadai da wannan mataki na shugaba Trump.

Bugu da kari, kasashen Canada, Burtaniya da Jamus da Faransa da Sweden da Switzerland da Naetherlands da Czech da sauransu su ma sun yi fatali da wannan mataki.

MDD da kungiyar tarayyar Turai EU da kungiyar hada kan kasashen Larabawa sun bi sahun kungiyoyin da ke Allah wadai da wannan mataki da Trump din ya dauka.

Ofishin Firaministar kasar Burtaniya Theresa May, ya bayyana cikin wata sanarwa a jiya Lahadi cewa, firaministar za ta sanya baki muddin wannan mataki ya shafi 'yan kasarta.

Shi ma firaministan kasar Canada Justin Trudean ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, kasar sa tana maraba da dukkan wadanda ke fuskantar barazana da musgunawa sakamakon wannan mataki na Trump, ba tare da la'akari da bambancin addini ko asali ba.

Haka zalika ministan harkokin wajen kasar Faransa Jean-Marc Ayrault ya fito karara yana watsi da matakin Trump, inda ya jaddada cewa, aikinsu shi ne maraba da 'yan gudun hijirar da suke gujewa yaki a kasashensu.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta yi Allah wadai da matakin shugaban na Amurka na haramtawa musulmi da 'yan gudun hijira shiga kasar na tsawon kwanaki 90,

Har wa yau, babbar jami'ar hukumar EU mai kula da manufofin diflomasiya da tsaro Federica Mogherini ta lashi takwabin cewa, hukumar za ta ci gaba da daukar matakan yin maraba tare da taimakawa 'yan gudun hijira daga kasashen da ake tabka yaki.

Shi ma babban sakataren kungiyar hada kan kasashen Larabawa Ahmed Aboul-Gheit ya bayyana rashin jin dadinsa game da matakin da shugaba Trump ya dauka, Don haka ya bukaci gwamnatin Amurka da ta sake nazartarsa, duba da yadda hakan ka iya yin illa ga jin dadin jama'a da kuma al'adu.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China